Bisa labarin da muka samu, an ce, a ran Lahadi 15 ga wata, yayin da yake tsokaci kan karin takunkumin da kasar Amurka ta kakabawa kasar Iran, ministan harkokin wajen kasar Iran Mohammad Javad Zarif ya bayyana cewa, tun lokacin da aka fara shawarwari kan batun nukiliyar kasar, ya fahimci cewa, shawarwarin abu ne mai wahala dake daukar dogon lokaci, kana kasar Iran za ta ci gaba da shawarwarin da take yi da kasashen nan shida dake shafar batun nukiliyar kasar.
Kan lamarin, Ms. Hua Chunying ta bayyana cewa, a halin yanzu, ya kamata bangarori daban daban da abin ya shafa su dukufa wajen warware batun nukiliyar kasar Iran ta hanyar shawarwarin siyasa bisa ka'idojin girmama juna da kuma nuna adalci ta yadda za a iya ciyar da wannan aiki gaba. (Maryam)