in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An fara sauraron tuhumar da ake yi wa Morsi a kasar Masar
2013-11-04 21:08:44 cri
Gidan talabijin na kasar Masar ya bayar da labarin cewa, yau ne a Alkahiri, babban birnin kasar ta Masar, aka fara sauraron tuhumar da ake yi wa shugaban kasar da aka hambarar Mohammed Morsi.

Da safiyar yau ne, aka kawo Morsi wanda ke da alaka da jam'iyyar 'yan uwa musulmi zauren kotun da ke Alkahira domin ya fuskanci tuhumar da ake masa ta tunzura tayar da hankali da kashe masu zanga-zanga, kara shiga fargabar yiwuwar tashin hankali a fadin kasar.

Ana zargin Morsi da wasu jiga-jigan 'yan uwa muslumi guda 14 da rura wutar tashin hankali da kashe masu bore a wajen fadar shugaban kasar a watan Disambar shekarar 2012.

Wannan shi ne karon farko da aka ga Morsi a bainar jama'a, tun lokacin da sojoji suka hambarar da shi a ranar 3 ga watan Yuli, don mayar da martani ga boren kasa baki daya da aka yi game da shugabancinsa na shekara guda, inda ake tsare da shi a wani wurin da ba a bayyana ba tun lokacin da aka kama shi.

Kamfanin dillancin labarai na kasar Masar MENA, ya bayyana cewa, an garzaya da Morsi ne ta jirgi mai saukar ungulu zuwa cibiyar horas da 'yan sanda da ke gabashin sabuwar gundumar birnin Alkahira, inda aka tsaurara matakan tsaro.

Sai dai alkalin da ke sauraron karar, ya bayyana cewa, an dage sauraran karar zuwa ranar 8 ga watan Janairun shekarar 2014.

Bayanai na nuna cewa, an dage sauraran karar ta yau ce har sau biyu, saboda wakokin da magoya bayan 'yan uwa musulmin ke rerawa na nuna kin amincewa kan kotun da kuma sojojin kasar.

Sai dai, Morsi ya shaidawa alkalan a karshen zaman kotun cewa, "Ni ne shugaban kasa, juyin mulkin da aka yi mini ya saba wa doka, kuma mummunan laifi ne, an kowa ni nan ne da karfi, ba bisa son raina ba", inda ya bukaci kotun da ta gurfanar da jagoran juyin mulki. (Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China