in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kwamitin koli na yin zaben kasar Masar ya yanke shawarar jinkirta lokacin yin zaben majalisar kasar
2013-03-08 14:51:59 cri
Bisa labarin da kamfanin dilancin labaru na Mena na kasar Masar ya bayar an ce, a ran 7 ga wata kwamitin koli na yin zaben kasar Masar ya yanke shawarar dage lokacin yin zaben majalisar wakilan kasar, amma yanzu ba a san hakikkanin lokaci da za a yi zaben ba.

Kwamitin ya ce, dalilin da ya sa yin hakan shi ne saboda kotu ta dage zaben majalisar dokokin a ran 6 ga wata, wanda shugaban kasar Mohamed Morsy ya yi shirin gudanarwa ran 22 ga watan Afrilu.

Kotun kasar Masar ta yi nuni a ran 6 ga wata cewa, yanzu an samu kararraki har guda 14 da aka gabatar dangane da daftarin sabuwar dokar  zaben majalisar dokoki. Kotun ta nemi a yi gyara ga wannan daftari kuma a mika shi ga babban kotun tsarin mulkin kasar don a dudduba shi.

Babban kotu ta yanke shawara a ran 18 ga watan Fabrairu cewa, wasu abubuwan dake cikin daftarin da majalisar dattijan ta gabatar sun sabawa tsarin mulkin kasar, saboda haka, ta mai da wannan daftari ga majalisar  domin yin gyare-gyare.

A ran 21 ga watan Fabrairu, majalisar dattijan kasar Masar ta karbi shirin da babban kotun ta gabatar dangane da yin gyare-gyare kan daftarin, wanda kuma ya samu amincewa daga Mohamed Morsy.

Bisa tanade-tanade dake cikin kundin tsarin mulkin kasar, ya kamata, majalisar dattajai ta gabatarwa babban kotu daftarin da ya yi gyara kansa.

Amma, a wanna karo, bai gabatarwa babban kotu ba, har sai da Mohamed Morsy ya sanar da yin zaben majalisar dokoki daga ran 22 ga watan Afrilu. (Amina)
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China