A yayin wani zaman taro da sojojin kasar suka shirya, mista Al-Sisi ya fada a gaban mahalarta taron cewa ba zai iyar juya baya ba ga kasar Masar.
Mista Al –Sisi ya yi amfani da wannan dama domin yin kira ga 'yan kasar Masar baki daya da su halarci zaben jin ra'ayi kan sabon kundin tsarin mulkin kasar da za'a shirya a ranakun 14 da 15 ga watan Janairu, tare da nuna cewa kundin na wakiltar kashi daya cikin kashi uku na sabon jadawalin tafiyar da mulkin kasar.
A karshe mista Al-Sisi ya nuna cewa idan har mutanen kasar Masar ba su harlarci wannan zaben raba gardama kan sabon kundin tsarin mulki sosai ba, to hakan zai kasance wani abun damuwa gare shi da kuma rundunar sojojin kasar. (Maman Ada)