in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Gwamnatin wucin gadin Masar ta ayyana kungiyar 'yan uwa Musulmi a matsayin kungiyar ta'addanci
2013-12-24 16:35:09 cri
A ranar 24 ga wata, kamfanin dillancin labaran kasar Masar MENA ya bayar da labari cewa, a wannan rana, firaministan gwamnatin wucin gadin kasar Masar Hazem el-Beblawi ya sanar da cewa, gwamnatin ta ayyana kungiyar 'yan uwa Musulmi a matsayin kungiyar ta'addanci.

Beblawi ya ba da wata sanarwa ta hannun mashawarcinsa a fannin yada labaru cewa, bayan da kungiyar 'yan uwa Musulmi ta haddasa rikicin zubar da jini, da kawo barna ga zaman lafiyan kasar, abun da ya nuna munanan ayyukanta na ta'addanci. Sanarwar ta ce, laifin ta'addanci da kungiyar ta aikata ba zai kawo cikas ga shirin mika da gwamnatin wucin gadin ta shirya ba, kana kuma, ba zai hana jama'a su shiga a dama da su a shirin tsara sabon daftarin tsarin mulkin kasar ba.

A shekarar 1928 ne, aka kafa kungiyar 'yan uwan Musulmi a Masar, kuma tarihi ya nuna cewa, hukumomin kasar sun sha rusa kungiyar. A watan Maris na bana, a matsayin kungiyar da ba ta gwamnatin ba, ta sake mai do da matsayinta a hukumance. Daga ranar 3 ga watan Yuli, bayan da aka tsige shugaba Morsi daga mukaminsa, magoya bayansa sun yi ta zanga-zanga, inda rikicin ya barke tsakaninta da sojoji, da 'yan sanda, da masu adawa da gwamnatin. Haka kuma, gwamnatin Masar ta cafke mambobin kungiyar 'yan uwan Musulmi da magoya bayan Morsi.

A ranar 9 ga watan Oktoba, gwamnatin Masar ta soke rajistar kungiyar 'yan uwan Musulmi, kuma ta hana aikace-aikacenta a kasar, gami da kwace dukkan kadarorinta. (Bako)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China