Mataimakin firaministan gwamnatin wucin gadi ta kasar Masar kuma ministan kula da harkokin bada ilmin jami'a na kasar Hossam Eissa ya sanar da wannan labari a gun taron manema labaru da aka gudanar a wannan rana. Kana ya bayyana cewa, za a ci gaba da daukar matakan kiyaye tsaro bayan da aka soke halin dokar ta baci.
A ranar 14 ga watan Agusta na bana, hukumar kasar Masar ta murkushe sansanin magoya bayan Mohamed Morsy, lamarin da ya kai ga aza dokar ta baci har na tsawon wata daya a dukkan kasar, tana kuma kafa dokar hana fitar dare tun daga karfe 7 na dare zuwa karfe 6 na safe a kowace rana a jihohi 14 na kasar. A halin yanzu, ana aiwatar da dokar hana fitar dare daga karfe 1 zuwa karfe 5 na safe a kowace rana. Amma dalilin yawan samun zanga-zanga bayan kowace sallar juma'a, sai lokacin dokar a juma'ar ya canja a ranar tun daga karfe 7 na dare zuwa karfe 5 na safe. (Zainab)