in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Manzon musamman na Sin ya yi kira ga bangarorin da abin ya shafa na Masar da su daidaita matsalarsu ta hanyar shawarwari
2013-12-04 11:00:04 cri

A ran 3 ga wata, manzon musamman na kasar Sin Mista Wu Sike yayi kira ga bangarorin da abin ya shafa na kasar Masar da su daidaita matsalarsu ta hanyoyin siyasa da shawarwari.

Mista Wu ya nuna cewa, ko kadan kasar Sin bata yarda da maida matsalar cikin gida ta kasar Masa a matsayin matsalar kasa da kasa. Kamata ya yi a bari gwamnatin kasar Masar da jama'arta su yi kokarin daidaita matsalar da kansu, a maimakon a bar kasashen waje su rika tsoma baki.

Game da dangantakar da ke tsakanin Sin da Masar, Mista Wu ya bayyana cewa, kasar Sin tana mai da hankali sosai kan raya dangantakarta tare da Masar. Ko wane irin sauyin yanayin duniya ba zai iya canza dangantakar abokantaka da hadin gwiwar kasashen biyu ba. Har kullum kasar Sin za ta kasance abokiya kuma 'yar uwa ga kasar Masar.

Mista Wu ya kai ziyara a Masar a ran 3 ga wata, inda ya gana da ministan harkokin waje na Masar Nabil Fahmy. A yayin ganawarsu, bangarorin biyu sun tattauna yadda za a raya dangantakar abokantaka da hadin kai a tsakaninsu da dabarun daidaita matsalolin shiyya-shiyya bisa sabon yanayin duniya, inda suka samu ra'ayi daya kan wasu batutuwa da dama.(Danladi)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China