Yayin da yake amsa tambayoyin manema labarai firaministan gwamnatin wucin gadi ta Masar, Hazem Beblawi ya ce makasudin wannan hari shi ne a tsorata fararen hula, tare da dasa shinge ga aikin gudanar da taswirar siyasa. Ya yi alkawarin kara kokari domin cafke wadanda suka tsara shirin da kuma gudanar da wannan danyen aiki. A sa'i daya, ya musunta cewa, gwamnatin wucin gadin kasar ta riga ta dauki kungiyar 'yan uwan Musulmi a matsayin kungiyar ta'addanci.
Kafin wannan, mai ba da shawara kan harkokin yada labaru na Hazem Beblawi, Sherif Shawky ya riga ya fidda sanarwar cewa, kungiyar 'yan uwan Musulmi kungiyar ta'addanci ce. Dadin dadawa, sanarwar ta kara da cewa, bayan haifar da rikicin zubar jini da lalata tsaron kasa, kungiyar ta fidda hakikanin fuskarta ta kungiyar ta'addanci.(Fatima)