A dai wannan rana gwamnatin kasar ta yi shelar dakatar da kaddarorin hukumomin gudanarwar kungiyar 'yan uwa Musulmi da sauran sassanta.
Bisa labarin da jaridar Al-Ahram ta Masar ta buga, an ce, magoya bayan kungiyar 'yan uwa Musulmin sun yi zanga-zanga a jihohi da dama, domin neman a maida shugaba Morsy kan mukamin sa na shugaban kasar. Masu zanga-zangar sun cunnawa motocin 'yan sanda wuta, lamarin da ya haddasa cunkoson ababen hawa a wurare da dama.
Bisa labarin da kamfanin dillancin labaru na MENA mallakar gwamnatin kasar Masar ya bayar, an ce, ma'aikatar harkokin cikin gidan kasar ta ba da sanarwar cewa, bisa shawarar da majalisar ministoci ta yanke, na ayyana kungiyar 'yan uwa Musulmi a matsayin kungiyar 'yan ta'addanci, za a yankewa membobin ta da aka cafke hukunci bisa tanajin doka.
Ma'aikatar harkokin cikin gidan kasar ta kuma yi shelar cewa, baya ga mutane 3 da suka rasu yayin tarzomar ta baya bayan nan, wasu jami'an 'yan sanda 4 sun jikkata, yayin da kuma aka kone motocin 'yan sanda 3. (Fatima)