in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ana fuskantar mawuyancin hali wajen samar da taimako jin kai a wannan shekara
2014-01-03 14:03:37 cri

Mataimakiyar direktar MDD mai kula da harkokin jin kai Madam Valerie Amos ta bayyana a ran 2 ga wata cewa, a wannan shekarar da muke ciki, MDD za ta dauki nauyin dake wuyanta na samarwa mutane fiye da miliyan 52 tallafin jin kai, matakin da yake bukatar dala biliyan 12.9.

A gun taron manema labaru da aka yi a wannan rana a birnin New York, Madam Amos ta yi bayani kan halin jin kai da ake fuskanta a bana, tana mai cewa, a shekarar da ta gabata, kasashen Sham, Afrika ta tsakiya, Philiphines sun fi fama da rikicin jin kai. Ban da haka, halin da Sudan ta kudu da Afrika ta tsakiya suke ciki wanda ya kara tsananta ya haddasa kara yawan 'yan gudun hijira.

Duniya na fuskantar wani rikici mai tsanani yanzu haka a wannan fanni, in ji Madam Amos, don haka ana bukatar karin kudi domin tinkarar rikicin jin kai dake bullowa nan gaba. A makonnin da suka gabata, rikicin Sudan ta kudu ya sa mutane dubu 194 sun yi gudun hijira, dubu 57 daga cikinsu na zaune a sansanin tawagar musamman na MDD. Ban da haka kuma, 'yan Afrika ta tsakiya dubu 800 da suka yi gudun hijira, kimanin dubu 500 na tsananin bukatar abinci.

Bugu da kari, Madam Amos ta yi bayani kan rikicin da ya barke a kasashen Kongo Kinshasa, Sudan, yankin Sahel, Afghanistan, Haiti da dai sauransu. Tana mai cewa, ya kamata, hukumomin dake kula da siyasa, cigaba, kiyaye zaman lafiya da jin kai su yi mu'ammala yadda ya kamata, ta yadda za su ba da taimako ga wasu kasashen da jama'arsu ke da bukata na dogon lokaci. (Amina)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China