Cikin sanarwar, kwamitin sulhu ya nuna bacin ransa matuka kan wannan harin ta'addanci, ya kuma nuna juyayi ga iyalan wadanda harin ya shafa. Bugu da kari, kwamitin sulhun ya sake jaddada cewa, kowane irin na'u'in harin ta'addanci yana daya daga cikin barazana mafi tsanani ga yananyin zaman lafiya da tsaro a duniya, ya kamata a hukunta masu aikata laifuffukan ta'addanci ba tare da tausaya musu ba.
Kwamitin sulhu na MDD ya sake jaddada cewa, ana bukatar a dukufa wajen yaki da aikace-aikacen ta'addanci wadanda suke kawo barazana ga zaman lafiya da tsaro a duniya yadda ya kamata, bisa kundin tsarin MDD da kuma dokokin kasa da kasa, musamman ma dokokin dake shafar harkokin hakin dan Adam, 'yan gudun hijira da kuma harkokin jin kai. Cikin sanarwar, kwamitin ya kuma jaddada babbar ka'idar ba dama a kai hari ga ofisoshin jakadancin kasa da kasa, da kuma harkokin da aka wajabtawa gwamnatocin kasa da kasa wajen kiyaye ofisoshin jakadancin kasashen waje. (Maryam)