Jiya Alhamis 24 ga wata rana ce ta MDD, wadda aka kebe domin bikin cika shekaru 68 da kaddamar da "kundin mulkin MDD", da kuma kafuwar MDD. Yayin zaman majalisar na 68, babban magatakardar majalisar Ban Ki-Moon, da shugaban babban taron majalissar karo na 68 Mr William Ashe, sun ba da jawabi a wannan rana, inda suka yi kira ga gamayyar kasa da kasa, da su yi hada kai da majalisar, wajen tinkarar kalubalolin dake addabar duniya baki daya.
A cikin jawabin sa, Ban Ki-Moon ya jaddada kalubalolin a yanzu haka ake fuskanta cikin gaggawa, ciki hadda burin samun ci gaba mai dorewa. Ya ce shirin cimma muradun karni ya riga ya yi nasara wajen rage rabin matalauta a duniya, don haka a cewarsa ya kamata a ci gaba da ba da himma a wannan fanni. Har ila yau Ban ya bukaci da a tsaida ajandar managartan ayyukan da majalisar za ta sanya gaba bayan shekarar 2015, domin kaiwa ga matsayin magance sauyin yanayi.
Bugu da kari, Ban ya ce MDD ta yi iyakacin kokari wajen warware batun rikice-rikice, ta hanyar dakile amfani da makamai, da kiyaye hakkin Bil Adam, muhalli da dai sauran ragowar batutuwa, a kokarinta na tabbatarwa jama'ar duniya ci gaba da aka samu cikin hadin gwiwa.
A nasa jawabi Mr William Ashe, cewa ya yi, tun kafuwar MDD a shekarar 1945, ta kasance wani dandali na jama'a dake wakiltar zaman lafiyar, da kare hakkin Bil Adam, ta kuma ba da jagoranci ga kasashen duniya cikin adalci.
Shekaru 68 da suka gabata ya zuwa yanzu duniya ta samu karin karfin tinkarar matsaloli sama da lokutan baya. Matakin da ake fatan zai ba da damar fuskantar kalubalolin dan adam irin daban-daban. (Amina)