in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Wakilin kasar Sin a MDD ya yi kira da a girmama hanyoyin raya hakkin bil'adama
2013-11-01 10:55:24 cri

Mataimakin zaunannen wakilin kasar Sin a MDD Mista Wang Min, ya bayyana a ranar 31 ga watan Oktoba cewa, samar da hakki ga dan Adam da kare shi, muhimmiyar manufa ce ga daukacin jama'ar duniya, amma babu wani tsari da ke iya samun karbuwa a ko ina, don haka kamata ya yi a girmama hanyoyin raya hakkin 'dan Adam da kasashen duniya daban daban ke bi bisa ga bukatun su.

Da yake tsokaci gaban mahalarta zaman kwamiti na uku, mai kula da harkokin da suka shafi zamantakewar al'umma, da jin kai na babban taron MDD kan batun hakkin dan Adam a ranar 31 ga watan Oktoba, Wang Min ya bayyana cewa, kamata ya yi kasashen yamma su girmama kokarin da ragowar kasashen duniya suke yi, musamman kasashe masu tasowa, wajen tabbatar da kare hakkin dan Adam bisa ga hakikanin halin da suke ciki. Yace ya zama wajibi kasashen yamma su yi cudanya, da hadin gwiwa da kasashen duniya kan batun kare hakkokin dan Adam, su kuma kawar da kuskuren da suke yi, na adawa da wadannan kasashe a siyasance.

Mista Wang ya ci gaba da cewa, gwamnatin kasar Sin ta gabatar da shawarar yin cudanya, da hadin kai kan batun kare hakkin dan Adam, tsakanin kasashen duniya. Za kuma ta aiwatar da yarjejeniyoyi 26, don tabbatar da kare hakkin dan Adam. Bugu da kari Wang, ya ce a ko wace shekara kasar Sin na yin shawarwari da kasashe wajen 20 kan wannan batu. Har ila yau Sin na hadin gwiwa da babban ofishi mai kula da hakkin dan Adam na MDD, da sauran hukumomi na musamman.

Sai dai duk da haka, minsta Wang ya bayyana cewa Sin, tana tsayawa tsayin daka wajen adawa da manufar kasashen yamma, dake tsayawa tamkar wasu malamai, dake da ikon zargin yadda ake kula da hakkin dan Adam a kasar ta Sin, ba tare da wani dalili ba. Yace a wannan lokaci da kasar Sin ke samun bunkasa, gwamnati za ta kara kyautata tsarin zamantakewar al'ummarta, tare da nuna fiffikon tsarinta, ta yadda za ta iya samun karin bunkasuwa a nan gaba.(Danladi)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China