A cewarsa, kasar Sin na kan gaba, wajen samar da gudummowa da yin hadin gwiwa da kasashe masu tasowa, don haka ta ba da taimako kwarai wajen tabbatar da ganin irin wadannan kasashe sun samu ci-gaba mai dorewa a nan gaba.
Haka zalika, Ashe ya kara da cewa, hadin kan kasahen dake samun saurin bunkasuwa a fannin na tattalin arziki a bangarorin cinikayya, da zuba jari, da musayar fasahohi ya kara habaka kokarin kasashe masu tasowar, wajen sauya salon tattalin arzikinsu. Ya ce, duk da cewa irin wadannan kasashe na fuskantar matsalolin da suka hada da talauci, da karancin abinci da tsaftataccen ruwa, da matsalar makamashi, da dai sauransu, a hannu guda matakan da suke dauka na amfani da sabbin fasahohi, da zuba jari, da gudanar da nagartattun manufofi za su sanya su samun damar warware matsalolin nasu yadda ya kamata. (Bello Wang)