An kira taro karo na 19 na kasashen da suka sanya hannu kan yarjejeniyar sauyin yanayi ta MDD, kuma taro karo na 9 na ministocin kasashen da suka sanya hannu kan yarjejeniyar Kyoto a jiya Talata 19 ga wata, a birnin Warsaw na kasar Poland.
Cikin jawabin da ya gabatar yayin bude taron, firaministan kasar ta Poland, kuma mai masaukin baki Donald Tusk, ya yi kira da dauki matakan samar da ci gaba yayin taron, yana mai cewa ya kamata, bangarori daban-daban sun yi iyakacin kokarin cimma matsaya guda.
Tusk ya kuma bayyana cewa, yayin taron za a gabatar da wata sabuwar hanyar kiyaye muhalli, ta yadda za a cimma matsaya daya kan yarjejeniyar yanayi.
Shi kuwa babban sakataren MDD Ban Ki-Moon, kira ya yi ga kasashe daban-daban, da su tinkari kalubalolin da sauyin yanayi ke janyowa, ta yin amfani da ilimi cikin gaggawa. Ban da haka, ya nemi wasu kasashe da su amince da alkawari karo na biyu, na yarjejeniyar Kyoto ba tare da bata lokaci ba.
Har ila yau Ban ya yi kira ga kasashe masu wadata, da su cika alkawuran da suka yi na samarwa kasashe masu tasowa kudi, da fasahohi a wannan fanni. (Amina)