in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin ta yi kira ga babban taron MDD da ta taka muhimmiyar rawa wajen tsara jadawalin ci gaba bayan 2015.
2013-12-05 10:12:52 cri
A ranar Laraban nan 4 ga wata, kasar Sin ta yi kira ga babban taron MDD da ta taka muhimmiyar rawa wajen tsara jadawalin ci gaban kasashen duniya bayan shekara ta 2015.

Wang Min, mataimakin wakilin kasar Sin na din din din a MDD ya yi wannan kira a lokacin da yake jawabi a zaman babban taro karo na 68 karkashin taken "farfado da ayyukan babban taron mu".

Mr. Wang ya lura da cewa, ganin yadda ake cikin wani yanayin na sarkakkiya, kasashen duniya suna da babban fata a kan Majalissar, musamman ma babban taron ta, wadda ita ce jagoran duk hukumomi na duniya.

Babban taron, in ji shi ya kamata ya mai da hankali a kan tattaunawa tare da tafiyar da manyan batutuwa da suka addabi kasashe mambobi, musamman wadanda suka shafi kasashe masu tasowa.

Duk da haka, in ji Mr Wang ya kamata babban taron majalissar ta karfafa shirin ta da kuma sauran hukumomin da ke karkashin ta bisa tsarin raba daidai na ayyuka domin kowa ya samu damar ba da nashi gudummuwa tare da inganta musayar bayanai da hulda a tsakani.

Wakilin na kasar Sin ya ci gaba da bayanin cewa, kasarsa tana goyon bayan ayyukan babban taron majalissar ta hanyar saukaka shawarwarin da za'a dauka da kuma inganta muhimmancin sa. (Fatimah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China