in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin ta yi hadin kai da kwamitin hakkin 'yan Adam na MDD
2013-10-23 10:52:00 cri

A ran 22 ga wata, kwamitin hakkin 'yan Adam na MDD ya kira taro a Geneva, don nazarin halin da ake ciki dangane da hakkin 'yan Adam a kasar Sin karo na biyu.

Shugaban tawagar kasar Sin, kuma manzon musamman daga ma'aikatar harkokin waje ta kasar Sin Mista Wu Hailong a cikin jawabin da ya gabatar ya yi bayani game da kokarin da kasar Sin ta yi a cikin shekaru 4 da suka wuce a fannonin kare hakkin 'yan Adam, da kuma matsalolin da kalubalen da take fuskanta. Mista Wu ya ce, a cikin shekaru 4 da suka wuce, kasar Sin ta fi mai da hankali kan samun bunkasuwa, ta kara kyautata zaman rayuwar jama'a, ta tabbatar da jama'a su ci moriya daga sha'anonin gayre-gyare da bunkasuwa. Ban da wannan kuma, kasar Sin ta gudanar da ayyuka da yawa don kare hakkin 'yan Adam musamman a fannonin tabbatar da ikon jama'a a fannin siyasa, da 'yancin fadin albarkacin bakinsu, da 'yancin addinai, da hakkin 'yan kananan kabilu da dai sauransu.

A tattaunawar da aka yi bayan jawabin tawagar kasar Sin, wakilai da suka zo daga kasashe 137 sun bayyana ra'ayoyinsu, inda yawancinsu musamman kasashe masu tasowa suka amince da kokarin da kasar Sin ta yi da kuma kyakkyawan sakamakon da ta samu wajen kare hakkin 'yan Adam a cikin shekaru 4 da suka wuce, kuma suka fahimci matsaloli da kalubalen da kasar Sin take fuskanta a matsayin kasar dake kan hanyar tasowa mafi girma, har wa yau kuma sun gabatar da wasu shawarwari masu yakini ga kasar Sin.(Danladi)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China