in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin za ta nace ga bin moriyarta mai tushe ba tare da kasala ba
2013-12-26 20:40:27 cri
Kwamitin tsakiya na jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin ta yi wani taro a ranar alhamis 26 ga wata a babban dakin taron jama'a dake birnin Beijing, fadar mulkin kasar, domin tunawa da ranar cika shekaru 120 da haifuwar babban jagoranta Mr Mao Zedong.

A lokacin taron babban sakataren kwamitin tsakiya na JKS kuma shugaban kasar Sin Mr Xi Jinping ya ba da jawabi inda ya ce tunanin Mao Zedong ya bayyana matsayin da Sin ke dauka wanda kuma ya kasu kashi uku, wato nacewa ga bin hakikkanin halin da ake ciki, yin hadin kai tsakanin jama'a da kuma dogaro da karfin kanta.

Yayin da ya tabo maganar dogaro da karfin kanta, Shugaba Xi ya ce, ya kamata, a aiwatar da manufar diplomasiyya bisa wannan ka'ida, da kuma bin hanyar samun bunkasuwa cikin lumana ba tare da kasala ba. Ban da haka, kamata ya yi, a yi tsaya tsayin daka kan ka'idoji biyar na yin zama tare cikin lumana, da kuma yin hadin kai bisa ka'idar kawo moriyar juna. Sannan kuma in ji shi a bi ka'idar kiyaye zaman lafiyar duniya gaba daya da sa kaimi ga samun bunkasuwa tare. Bugu da kari a tsai da manufofi bisa adalci, daidaici, sannan da mutunta hanyoyin da jama'ar sauran kasashen suka zaba wajen samun bunkasuwa.

Shugaban na Sin ya kuma ce kasar ba za ta amince da ko wani mataki da sauran kasashe za su dauka ba na matsa lamba kan jama'ar kasar Sin da tsoma baki cikin harkokin cikin gidanta. Sannan ya jaddada matsayin da Sin ke dauka na warware rikici ta hanyar lumana. (Amina)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China