in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban kasar Sin ya gana da shugaban kwamitin wasannin Olympics na duniya Thomas Bach
2013-11-20 10:56:35 cri
A ranar Talata 19 ga wata, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gana da shugaban kwamitin wasannin Olympics na duniya Thomas Bach a nan birnin Beijing, inda ya jaddada cewa, kasar Sin ta dora muhimmanci game da raya wasannin motsa jiki, da kuma irin muhimmiyar rawa da wasannin Olympics ke takawa wajen raya zamantakewar al'umma.

Ya ce, a cikin 'yan shekarun nan, Sin ta shirya gasar wasannin Olympics ta Beijing, da gasar wasannin Paralympics ta Beijing da gasar wasannin Asiya ta Guangzhou da sauran wasannin kasa da kasa, kuma kasar Sin in ji shi za ta bi manufar da aka tsara a gun cikakken zaman taro na uku na jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin karo na 18, don kara kokari wajen kyautata lafiyar jikin jama'a, da raya wasannin motsa jiki.

Shugaba Xi ya yi bayanin cewa, a watan Agusta na shekara mai zuwa, za a yi gasar wasannin Olympics ta matasa a birnin Nanjing da ke kasar Sin, kuma an riga an kimtsa yadda ya kamata.

Haka kuma, birnin Beijing da na Zhang Jiakou sun gabatar da rokon shirya gasar wasannin Olympics karo na 24 a lokacin sanyi a shekarar 2022. Kasar Sin tana fatan yin amfani da wannan dama, don yalwata wasannin Olympics da ayyukan wasannin da aka yi su a lokacin sanyi.

A nashi bangaren shugaban kwamitin wasannin Olympics na duniya Thomas Bach ya jinjina ma gwamnatin kasar Sin game da goyon baya da ta ke yi ga wasannin Olympics na duniya. Yana mai cewa, kasar Sin ta ba da babbar gudummawa game da raya wasannin duniya. An shirya gasar wasannin Olympics ta Beijing da cikakkiyar nasara, kuma abin da ya kawo ma duniya alheri sosai. Bach ya kara da cewa, dalilin da ya sa ya zabi kasar Sin don ta zama kasa ta farko da zai ziyarta, bayan ya zama shugaban kwamitin wasannin Olympics na duniya, shi ne domin nuna fatan kwamitin din na inganta hadin gwiwa da kasar Sin.

Daga bisani, a madadin kwamitin wasannin Olympics, Thomas Bach ya ba da lambar yabo ta zinariya ta Olympics ga shugaba Xi Jinping, don jinjina kokarin da ya yi wajen sa kaimi ga raya wasannin motsa jiki da raya akidar Olympics.(Bako)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China