in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban kasar Sin ya gana da tsohun shugaban kasar Amurka
2013-11-18 16:08:14 cri

Yau Litinin 18 ga wata, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gana da tsohun shugaban kasar Amurka Bill Clinton a nan birnin Beijing. A lokacin ganawar, Mr Xi ya nuna cewa, shi da shugaban kasar Amurka Barack Obama sun cimma matsaya daya kan raya sabuwar dangantakar dake tsakaninsu tare. Yace ya kasance manufa da bangarorin biyu suka tsayar bisa moriyar kasashen biyu da jama'arsu, don haka Sin da Amurka na da makoma mai haske a wannan fanni, idan sun nace ga raya irin wannan dangantaka bisa ka'idar mutunta juna da kawo moriyar juna.

Mr Xi ya bayyana cewa, raya irin wannan dangantaka na bukatar mutanen sassa daban-daban na bangarorin biyu da su ba da gudunmawarsu, don haka, yana fatan Mr Clinton da asusunsa za su ba da taimako, ta yadda za a sa kaimi ga mutane da dama da su shiga aikin habaka hadin kai tsakanin bangarorin biyu.

A nasa bangare, Mr Clinton ya nuna cewa, ya kamata, kasashen biyu sun kara hadin kai tsakaninsu da kuma tinkarar kalubaloli daban-daban tare, ta yadda za a shimfida wani yanayi mai kyau ga jama'arsu nan gaba. Shi da asusunsa za su sa kaimi ga bangarorin biyu da su yi hadin kai a fannonin kiwon lafiya, sabbin makamashi, kiyaye muhalli, sauyin yanayi da sauransu, kuma za su yi hadin gwiwa da kasar Sin a Afirka da sauran nahiyoyin duniya, ta yadda za su sa kaimi ga samun zaman alherin jama'a da bunkasuwar duniya mai dorewa. (Amina)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China