Shugaban kasar Sin Mr. Xi Jinping, ya bayar da umarni da a duba matakan da kamfanoni ke dauka wajen kula da lafiyar ma'aikatansu, ta yadda za su koyi darasi daga fashewar da ta faru ranar Jumma'a sakamakon yoyon wani bututu.
Shugaba Xi Jinping ya yi wadannan kalamai ne a birnin Qingdao da ke lardin Shandong na kasar Sin, bayan da ya ziyarci wurin da aka samu wata fashewa a sakamakon yoyon gurbataccen danyen mai daga wani bututu, lamarin da ya yi sanadiyar mutuwar mutane 52.
Ya ce, hadarin da ya faru, wata manuniya ce ta bukatar masana'antu su kara daukar matakan da suka dace na hana abkuwar hakan nan gaba tare da gujewa kasar da jama'a fadawa mummunar asara.
Shugaba Xi ya kuma jadadda cewa, kamata ya yi a hanzarta gudanar da bincike, a kula da wadanda lamarin ya rutsa da su kamar yadda doka ta tanada, kana ya jajantawa iyalan wadanda lamarin ya shafa.
Daga bisani a ranar Lahadi da rana, shugaba Xi ya ziyarci wasu mutanen da suka ji rauni da ma'aikatan kiwon lafiya da ke aiki a reshen asibitin Huangdao wanda ke karkashin kwalejin koyon aikin likita ta jami'ar Qiangdao. (Ibrahim)