in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Xi Jinping ya gana da firaministan kasar Ingila
2013-12-02 20:28:32 cri

Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gana da firaministan kasar Ingila David Cameron‎ a yau Litinin 2 ga wata a nan birnin Beijing.

A yayin ganawar, Xi Jinping ya jaddada cewa, kamata ya yi kasashen biyu su yi hangen nesa, daidaita bambance-bambancen dake tsakaninsu kan yanayin kasa da tsarinsu, kara fahimtar juna, girmama da juna, sa lura kan abubuwan da suke kulawa, tsara makomar dangantakarsu, da kuma sa kaimi ga yin hadin gwiwa a tsakaninsu yadda ya kamata.

Kana Xi Jinping ya nuna cewa, yanzu Sin tana aiwatar da ayyukan da aka tsara a gun cikakken zama karo na 3 na kwamitin tsakiyar JKS na 18, da yin kwaskwarima da bude kofa, canja hanyoyin bunkasa tattalin arziki, kyautata tsarin tattalin arziki, da kuma sa kaimi ga kamfanonin Sin da su gudanar da cinikayya a kasashen waje. Kamata ya yi kasashen biyu su kara yin hadin gwiwa a wannan lokaci. Ban da wannan kuma, ya kamata kasashen biyu su kara yin mu'amala kan harkokin kasa da kasa, da bin ra'ayin raya dangantaka a tsakanin kasa da kasa cikin lumana, da samun bunkasuwa, hadin gwiwa, da kuma moriyar juna don tinkarar kalubalen da ake fuskanta a duniya gaba daya.

A nasa bangare, Mr Cameron ya bayyana cewa, an tsara makomar bunkasuwar kasar Sin a gun cikakken zama karo na 3 na kwamitin tsakiyar JKS na 18, wannan ya jawo hankalin kasa da kasa sosai. Kana ya yi imani cewa, kasar Sin za ta cimma burinta, kuma yana fatan kara ganin ayyukan yin kwaskwarima da bude kofa a kasar Sin. Kuma kasar Ingila ta dora muhimmanci sosai kan nasarorin da Sin ta samu da kuma hadin gwiwar dake tsakanin Ingila da Sin. Ingila tana son kara yin mu'amala tare da kasar Sin kan manyan batutuwan kasa da kasa da shiyya-shiyya, da tabbatar da zaman lafiya da na karko a duniya, da kuma sa kaimi ga farfado da tattalin arzikin duniya da samun bunkasuwa mai dorewa. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China