in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin da Amurka za su inganta tsare-tsarensu a tsakaninsu, in ji Xi Jinping
2013-11-15 20:46:47 cri

Kasashen Sin da Amurka ya kamata su inganta dangantakar tsare-tsare a tsakaninsu lokacin da suke gudanar da ayyukan kwaskwarima da yin gyare gyare, in ji shugaban kasar Sin Xi Jinping.

Shugaba Xi ya fadi hakan ne a yau Jumma'a 15 ga wata a lokacin ganawarsa da wakilin shugaban kasar Amurka Barack Obama, ministan kudi na kasar Amurka Jacob Lew a nan birnin Beijing.

Mr. Xi ya ce, cikakken zama karo na uku na kwamitin tsakiyar JKS na 18 da aka kammala a kwanan nan ya mai da muhimmanci a kan yin gyare-gyare kan tattalin arziki, kuma Sin za ta yi kokarin ingiza ayyukan kwaskwarima cikin kwazo tare da ci gaba da rike matsayin ci gaba mai yakini na tattalin arziki.

Shugaba Xi ya yi bayanin cewa, kasar Sin tana fatan Amurka za ta inganta nata kwaskwarimar domin cimma madafa da kuma tsayawa a kan farfadowar tattalin arziki mai ci gaba.(Fatimah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China