A ranar Alhamis ne shugaban kasar Mr. Xi Jinping, ya bayyana muhimmancin nuna daidaiton jinsi, inda ya yi kiran da a baiwa mata cikakkiyar damar taka rawa, ta yadda za su taimaka wa kasar ta Sin cimma nasarar manufofin da ta sanya a gaba.
Shugaba Xi ya bayyana hakan ne, yayin wata ganawa da sabbin shugabannin tarayyar kungiyoyin matan kasar da aka zaba.
Ya ce, a 'yan shekarun nan, Sin tana dora muhimmanci sosai ga batun nuna daidaiton jinsi a dukkan harkokin ci gaba. Yana mai cewa, Sin na fuskantar karin kalubale a bangaren tattalin arziki da bunkasa jin dadin jama'a, saboda haka, shugaban na Sin ya ce, kasar tana bukatar karin gudummawa da hikima daga mata fiye da lokutan baya.
Shugaba Xi ya yi kiran da a hade tsare-tsaren raya kasar da batun yayata daidaiton jinsi, matakin da shugaban ya ce, zai bai wa matan damar bayyana 'yancin da suke da shi a tsarin demokiradiya kamar yadda doka ta zayyana, shiga harkokin tattalin arziki da bunkasa jin dadin jama'a, kana su ci gajiyar kwaskwarimar da aka aiwatar.
Bugu da kari, shugaban na Sin, ya yi kira ga jami'an tarayyar kungiyoyin matan a dukkan matakai, da su kara gano halin da ake ciki a yankunan karkara, ta yadda za a inganta rayuwar mata. (Ibrahim)