Mista Xi ya yi wannan kashedi a cikin wani umurnin a rubuce kan aiki da yaki da Sida a kasar Sin a jajibrin ranar duniya ta yaki da cutar Sida dake gudana ko wace ranar daya ga watan Disamba.
A cewar mista Xi, yin rigakafi da sanya ido kan wannan annoba na shafar rayuwa da lafiya al'ummar kasa, har ma zaman jituwa da kwanciyar hankalin jama'a, kuma na kasancewa wani nauyin da ba na wasa ba ga jam'iyyar Kwaminis ta kasar Sin da gwamnatin kasar Sin.
Shugaba Xi Jinping ya bukaci jam'iyyar da hukumomin gwamnatin daga dukkan bangarori da su kara azama wajen yaki da cutar Sida.
Da yake bayani kan rahoton da aka gabatar wa kwamitin tsakiya na jam'iyyar Kwaminis ta kasar Sin da ya shafi da'irar birnin Beijing kan aikinsa na yaki da cutar Sida, mista Xi ya nuna yabo sosai kan ci-gaban da aka samu a babban birnin kasar Sin a wannan fanni tare kuma da yin kira ga hukumomin birnin da su dukufa yadda ya kamata wajen gabatar da sakamako na kwarewar da suka samu domin cimma wasu sabbin ci-gaba a wannan fanni na yaki da Sida. (Maman Ada)