in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kamata ya yi a kara kokarin yin kwaskwarima, in ji shugaban kasar Sin
2013-11-28 19:53:01 cri

Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya ce, zurfafa yin kwaskwarima a dukkan fannoni na da muhimmanci kwarai wajen raya kasar mai zaman wadata da bunkasa al'ummar kasar, kuma ya zama tilas kwamitocin JKS na matakai daban daban su mai da hankali kan wannan aiki, su sauke nauyi yadda ya kamata, a kokarin gudanar da manufofin da kwamitin tsakiyar JKS ya gabatar yadda ya kamata.

Daga ranar 24 zuwa 28 ga wata, shugaba Xi ya yi bincike kan yanayin da ake ciki a lardin Shandong a fannin bunkasa tattalin arziki da zamantakewar al'umma, inda ya bayyana cewa, kamata ya yi dukkan membobin JKS su kara kwarin gwiwa wajen tabbatar da shirin yin kwaskwarima, da fatan kowa zai kara fahimta, da nuna goyon baya, da kuma shiga aikin domin a yi tare da shi.

Ya ce, wajibi ne a gudanar da wannan aiki yadda ya kamata tare da samun daidaito tsakanin bangarori daban daban, da dora muhimmanci kan alakar yin kwaskwarima, tare da kokarin gudanar da manyan manufofin kwamitin tsakiyar JKS cikin yakini.(Fatima)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China