in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Xi Jinping ya dawo kasar Sin bayan halartar kwarya-kwaryar taron APEC
2013-10-08 16:46:56 cri

Bayan halartar babban taron na karo 21 na shugabanni kungiyar APEC a tsibirin Bali na kasar Indonesiya, shugaba Xi Jinping na kasar Sin ya tashi daga tsibirin a ran 8 ga wata da yamma don dawo kasar.

Babban take na taron Bali shi ne, 'a wadatar da yankin Asiya da Tekun Pacific, ta yadda zai iya ba da taimako ga bunkasuwar duk duniya', inda aka tattauna kan shirin muradun Bogor, wato muradun da aka tsara a garin Bogor na Indonesiya a shekara ta 1994 da zai samar da bunkasuwa cikin dogon lokaci da adalci, da kuma kara sadarwa a tsakanin kasashen Asiya da Tekun Pacific da dai sauransu.

Haka kuma shugabannin da suka halarci taron sun yi musanyar ra'ayoyinsu kan halin tattalin arziki na duniya da shiyyar da APEC ke ciki. Kafin ya halarci taron tsibirin Bali, shugaba Xi ya kai ziyarar aiki a kasashen Indonesiya da kuma Malasiya.(Danladi)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China