Bisa kididdigar da aka bayar an ce, a watan Nuwamba na shekarar bana, yawan kudin da aka kashe wajen sayen abubuwan yau da kullum ya kai RMB Yuan biliyan 2101, wanda ya karu da kashi 13.7 cikin dari bisa ga makamancin lokacin shekarar bara.
Dadin dadawa, an ba da labari cewa, a watan Nuwanba, yawan kudin da aka kashe a fannin gidaje da harkokin sufuri ya karu sosai. Ban da haka, Hukumar cinikayya ta ba da wani rahoto bisa ga kamfanoni 3000 da ta yi bincike kansu, yawan kudin da kamfanonin samar da na'urorin yau da kullum da kamfanonin kayayyakin amfanin gidaje suka samu ya karu da kashi 16.2 ciki dari da kashi 14.6 cikin dari. Sana'ar motoci kuwa na samun karuwa sannu a hankali.
Hukumar ta yi kiyasin cewa, kasuwar ciniki a kasar Sin za ta kara saurin karuwa nan gaba dalilin halin da ake ciki a fannin harkokin sayyaya a kasar. (Amina)