Kafin wannan, kakakin ma'aikatar harkokin kasuwancin kasar ta Sin Shen Danyang ya bayyana cewa, bisa shiri na 12 na raya kasar ta Sin cikin shekaru biyar biyar, ana sa ran ganin a cikin ko wace shekara adadin karuwar cinikayyar shigi da fici ya kai kashi 10 bisa dari, kuma cikin shekaru biyu da suka gabata, an cimma nasarar wannan buri da adadin da ya kai kashi 14%, sa'an nan kuma, cikin farkon rabin shekarar bana, an an samu karuwar da ta kai kashi 8.6 bisa dari kan wannan fanni, watau ke nan matsakaicin adadin cikin shekaru biyu da rabi da suka gabata ya riga ya wuce burin da aka tsara. Bugu da kari, bisa hasashen da ma'aikatar harkokin kasuwancin kasar ta yi, an ce, kila ne yawan cinikayyar shigi da fici da kasar Sin ke yi da kasashen duniya zai kasance na farko a duniya a shekarar bana. (maryam)