Rahoton ya yi nazarin cewa, tun shekarar 2013, yanayin tattalin arziki na gida da na ketare ya shiga wani mawuyacin hali, wato, cikin farkon rabin shekarar bana, ba a tabbatar da karkon karuwar yawan hajjojin da aka fitar zuwa ketare da kuma wadanda aka shigo da su daga ketare ba, sakamakon haka, gwamnatin kasar Sin ta fidda wasu manufofi don tabbatar da karkon karuwar yanayin kasuwanci na kasar, da kyautatta tsarin tattalin arziki, ta yadda aka baiwa kamfanoni goyon baya da kuma inganta bunkasuwar kasuwancin ketare.
Bugu da kari, cikin karshen watanni 3 na shekarar bana, za a ci gaba da samun karkon karuwar yanayin kasuwancin ketare, kuma bisa hasashen da aka yi, gaba daya yawan kason da kasar Sin za ta samu bisa na duniya wajen fitar da hajjoji zuwa ketare zai iya karuwa kadan a shekarar bana.
Cikin 'yan shekaru nan, bayan da kasar Sin ta kasance ta farko a duniya wajen fitar da hajjoji, yawan kason da Sin ta samu a wannan fanni shi ma ya karu, ya zuwa shekarar 2012, ya kai kashi 11 bisa dari na jarin kasa da kasa.
Rahoton ya kuma nuna cewa, ko da za a iya samun kyautattuwar yanayin kasuwancin ketare a shekarar 2014, akwai kalubaloli da dama da za a gamu da su, kana, sabo da wasu manufofin bunkasa kasuwancin ketare da kasar ta fito da su, babu shakka za a tabattar da karuwar aikin a shekara mai zuwa. (Maryam)