Firaminista Li ya ce, yanzu ana yin kwaskwarima kan tsarin tattalin arzikin duniya, a bayyane yake ana fuskantar koma baya, a sa'I daya kuma ana fuskantar manyan kalubale. Kasa da kasa suna mai da hankali sosai kan farfado da tattalin arziki, amma ba kasar da za ta gudanar da wannan aiki da kanta. Kamata ya yi kasashen duniya su karfafa hadin gwiwa tsakaninsu, tare da samun moriyar juna. Da fatan dandalin tattaunawa kan tattalin arzikin duniya zai taka rawar a zo a gani wajen sa kaimi ga samar da yanayi mai 'yanci ga cinikayya da zuba jari na duniya baki daya.(Fatima)