in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Cinikayyar shige da fice ta kasar Sin ta samu karuwa a watan Afrilu da ya gabata
2013-05-09 16:47:05 cri

Hukumar kwastan ta kasar Sin ta fidda wata kididdiga a ran 8 ga watan nan, mai nuna cewa, cinikayyar shige da fice ci gaba da farfadowa tun karshen shekarar bara, kuma a watan Afrilu da ya gabata, yawan kayayyaki da Sin ta fitar zuwa kasashen waje ya kai kashi 14.7 bisa dari, yayin da yawan kayayyakin da Sin ta shigo da su ya karu da kashi 16.8 bisa dari.

A cikin farkon watanni hudu na bana, manyan ma'aunai uku; wato jimillar cinikayyar shige da fice, da adadin kayayyakin da Sin ta fitar zuwa kasashen waje, da kuma adadin kayayyakin da Sin ta shigo da su sun samu karuwa da ya haura kashi 10 cikin dari, abin da ya wuce yadda aka yi tsamani. Cinikayyar shige da fice ta ci gaba da samun bunkasuwa tun karshen watanni uku na shekarar bara, ana kuma fatan za ta ci gaba da samun bunkasuwa mai karko.

Lardin Guangdong dake dab da teku, wanda ya kasance wani lardin mafi dake kan gaba wajen fitar da kayayyaki zuwa kasashen waje, ya samu karuwa ta fiye da kashi 30 bisa dari, yayin da a lardunan Zhejiang, da Shandong, da kuma Fujian, aka samu karuwa fiye da kashi 7 bisa dari. Har ila yau, wasu yankuna dake tsakiya da yammacin kasar Sin, su ma sun samu bunkasuwa yadda ya kamata a wannan fanni, inda yawan karuwa da larduna Anhui, Jiangxi, da Sichuan suka samu ya kai fiye da kashi 30 bisa dari.

Kakakin babbar hukumar kwastan ta kasar Sin Zheng Yuesheng ya nuna cewa, za a ci gaba da samun bunkasuwa a wannan fanni, musamman ganin cewa, tattalin arziki a cikin gida na samun bunkasuwa yadda ya kamata, da kuma kwarin gwiwar 'yan kasuwa na inganta. Saboda haka, a takaice dai, yanayin cinikayyar shige da fice da Sin take ciki a bana, na nuna cewa kila za ta samu karin kyautatuwa fiye da shekarar bara. (Amina)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China