in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An kadadmar da yankin cinikayya cikin 'yanci na gwaji a birnin Shanghai na kasar Sin
2013-09-29 16:44:16 cri

Yau Lahadi 29 ga wata da safi ne aka kaddamar da yankin cinikayya cikin 'yanci na gwaji a yankin Pudong, dake birnin Shanghai na kasar Sin. Haka nan kuma an gudanar da ayyukan gwaje-gwaje da suka shafi wannan yanki.

Wannan biki dai ya kasance wani muhimmin mataki ne na ingiza tsarin yin kwaskwarima, da bude kofa ga kasashen waje, wanda ya zo kafin kiran cikakken zama na 3 na kwamitin tsakiyar jam'iyyar kwamins ta Sin a karo na 18.

Sakataren kwamitin Shanghai, kuma wakilin dindindin a kwamitin tsakiyar jam'iyyar kwaminis ta Sin Han Zheng, da ministan kasuwancin kasar Sin Gao Hucheng, da mataimakin sakataren kwamitin Shanghai, kuma shugaban birnin Shanghai Yang Xiong, na cikin manyan jami'ai da suka halarci wannan biki. Ban da haka, wakilan kamfanoni na gida da na waje fiye da dari, su ma sun shaida wannan lamari.

A wannan rana kuma, kamfanoni na gida da na waje 25, da kungiyoyin hada-hadar kudi na gida da na waje 11 ne suka shiga wannan yanki.

An ba da labari cewa, a watan Agustan bana ne majalissar gudanarwa ta kasar Sin ta amince da kafa wannan yanki a birnin na Shanghai, wanda ya shafi yankuna hudu na musamman, da hukumar kwastan ke kulawa da su, kuma fadin yankin ya kai murabba'in kilomita 28.78.

Babban aikin wannan yanki shi ne kara saurin gyara ayyukan gwamnatin, da habaka zuba jari, da ingiza canja hanyar samun bunkasuwa, da zurfafa bude kofa, da bunkasa fannin hada-hadar kudi, da ba da tabbaci ga shari'a da doka a wannan fanni. A sa'i daya kuma, yankin na dukufa kan samar da wani yanayi mai kyau ta fuskar sa ido ga buga haraji.

An ba da labari cewa, ayyukan da za a gudanar cikin yankin za su kunshi bangarori shida, da suka hada da hada-hadar kudi, da zirga-zirgar teku, da harkokin cinikayya, ba da hidima a fannin al'adu ga al'umma da dai sauransu. (Amina)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China