Rahotannin baya bayan nan na nuna cewa matsayin kudin Sin RMB na daguwa a fannin hada-hadar cinikkayar kasa da kasa cikin sauri.
Kungiyar sadarwa ta hadakar bankuna karkashin bankin duniya ko SWIFT a takaice, ta fidda wani rahoto dake cewa, a watan Oktobar bana, karkashin yarjeniyoyin da aka daddale dangane da ba da rancen kudi a fannin cinikayyar kasa da kasa, yawan kudin Sin da aka yi amfani da shi ya karu zuwa kashi 8.66 cikin dari, daga kashi 1.89 cikin dari a watan Janairun shekarar bara.
Haka zalika kudin Sin ya kai matsayi na biyu a duniya baya ga dalar Amurka, a fannin hada-hadar kudin cinikayyar kasa da kasa.
Bisa kididdigar da aka fitar an ce, yanzu kudin da aka fi yawan amfani da shi a cinikayyar kasa da kasa shi ne dalar Amurka, wanda yawansa ya kai kashi 81.08 bisa dari, yayin da kason kudin Euro ya ragu zuwa kashi 6.64 bisa dari, wanda ya sanya shi zama a matsayi na uku a duniya. (Amina)