A shekarar 2014, babban aiki da za a gudanar a fannin tattalin arziki, shi ne yin gyare-gyare, ta hanyar zurfafa sabbin matakan raya tattalin arziki da zamantakewar al'umma. An kaddamar da wannan batu ne, yayin taron cikakken zama na 3 na jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin karo na 18, inda aka gabatar da ajandar aikin yin gyare-gyare, kuma abin da zai sa kaimi ga kasar Sin da kasashen duniya su hada kai wajen samun moriyar juna tare.(Bako)