A cewar del Buey, jimillar da aka daidaita ta nuna yadda aka samu ci gaba wajen shiga cikin yankin arewacin kasar Mali, gami da yadda ayyuka suka samu gyaruwa a fannin kidayar mutanen da suka yi gudun hijira a Bamako, fadar mulkin kasar.
A watannin da suka gabata, MDD ta sanar da damuwarta wajen gano karin masu tsattsauran ra'ayi a kasar Mali, da cin zarafin mutane, da tsananin talauci da suka yi katutu a kasar. Ban da haka, an ba da rahotanni kan yawan gano fasa kwaurin makamai, da miyagun kwayoyi, har ma fataucin mutane da aka yi a arewacin kasar Mali.
Kakakin MDD ya ce, jimillar da majalisar ta gabatar ta sheda karin mutanen da suka yi gudun hijira sakamakon rashin kwanciyar hankali, da cigaba da cin zarafin jama'a a arewacin kasar Mali, gami da tsoron matakan soja da za'a iya dauka, da karancin abubuwan amfanin yau da kullum da na more rayuwa.(Bello Wang)