A wannan rana kuma, ofishin kyautata harkokin jin kai na MDD dake karkashin jagorancin madam Amos ya bayyana cewa, a sakamakon rikice-rikicen da suka abku a jihohin South Kordofan da Blue Nile na kasar Sudan, 'yan gudun hijira da yawa sun sheka cikin kasar Sudan ta Kudu a cikin 'yan kwanakin da suka wuce.
A game da wannan matsala, madam Amos ta furta cewa, mutanen Sudan kimanin dubu 170 sun bar gidajensu a sakamakon rikice-rikice da matsalar karancin abinci. Kuma mutanen da suka gudu zuwa kasar Sudan ta Kudu, bayan zuwansu a kasar, sun shiga cikin wani halin kaka-nika-yi. Mutane da yawa sun mutu a sakamakon kamuwa da cututtuka, dalilin rashin samun kulawa.
Bisa labarin da aka bayar, an ce, an shelanta kebe wannan kudi daga asusun daidaita matsaloli cikin gaggawa na MDD a wannan rana. An yi kiyasin cewa, 'yan gudun hijira kimanin dubu 65 za su ci gajiyar wannan taimako.(Fatima)