Yanzu wadannan jami'ai 2 suna nan suna ziyara a Lebanon, inda suka yi shawarwari da Najib Mikati, firaministan kasar. Bangarorin 3 sun ba da muhimmanci kan tattauna halin da ake ciki a fannin tinkarar matsalar Sham, musamman ma matsalar jin kai da 'yan gudun hijira na kasar suke fuskanta da kuma bai wa Lebanon tallafi da dai sauransu.
Jami'an 2 sun nuna cewa, ya kamata kasashen duniya su hada kai da kasashen da suka tsugunar da wadannan 'yan gudun hijira yadda ya kamata, su kuma share fagen tinkarar matsanancin halin da za a fuskanta a nan gaba. (Tasallah)