Hukumar kula da harkokin 'yan gudun hijira ta MDD ta sanar a ran 31 ga watan Mayu a birnin Geneva cewa, an kara yawan kudin da aka shirya tattarawa domin taimakawa yankin Sahel na Afrika a wannan shekara daga dalar Amurka miliyan 35 da dubu 600 da aka bayar a watan Fabrairu zuwa dala miliyan 153 da dubu 700, za a yi amfani da wadannan kudade wajen taimakawa 'yan gudun hijira na kasar Mali da kuma wadanda suka tsira zuwa kasashen dake makwabtaka da kasar.
Hukumar ta bayyana cewa, yanzu, yawan 'yan gudun hijira na kasar Mali ya ninka sau 5 idan aka kwatanta da adadin da aka kiyasta a watan Faburairu na wannan shekara. Karin kudaden da aka shirya tattarawa za su taimakawa 'yan gudun hijira dubu 240 na kasar Mali da suka shiga kasashen dake makwabtaka da ita da kuma mutane dubu 200 da ba su da gidajen kwana na cikin kasar. Ya zuwa yanzu, hukumar ta samu kashi 13 cikin dari kawai na daukacin kudaden da take bukata.
Bugu da kari, hukumar ta bayar da rahoto kan 'yan gudun hijira na duniya a wannan rana, inda aka yi hasashe cewa, za a fuskanci karin kalubale a fannin 'yan gudun hijira na duniya. Rahoton ya ce, kashi 80 cikin 100 na'yan gudun na duniya sun kasance a kasashe masu tasowa ne, ya kamata gamayyar kasa da kasa su kara yin hadin gwiwa domin tinkarar wannan matsala.(Lami)