Lamarin jin kai a jihar Blue Nile ta kasar Sudan ya kasance cikin wani mawuyacin hali da ke ci gaba da tabarbarewa, a yayin da mutane kimanin dubu 35 'yan gudun hijira ke isa a yankin na Blue Nile a cikin sati 3 na baya bayan nan. Fadan da ke gudana tsakanin dakarun gwamnatin kasar Sudan da dakarun kungiyar 'yan tawaye ta Arewacin kasar shi ne ya haddasa lamarin.
Tun da farko akwai 'yan gudun hijira dubu 70 da kuma yanzu wadannan sabbin zuwa suka karu a kan su a cikin wannan yanki. Hukumar kula da 'yan gudun hijira ta MDD ta gaggauta yin tsokaci kan wannan tururuwa ta 'yan gudun hijira.
A cewar Mista Guterres, wannan sabon canji ne a cikin yanayi jin kai da ya kasance mawuyaci tun can da farko.Ga shi dai yawan 'yan gudun hijira ya karu da dama, kuma yanayin ya kasance ba shi da kyau kwarai da gaske. Mutane da dama sun ci ganyen itace a kan hanya domin su rayu.(Abdou Halilou)