Madam Joyce, wakiliyar hukumar UNHCR da ke kasar Zambia ta bayyana a yayin wani babban taron da aka shirya don tunawa da ranar 'yan gudun hijira ta duniya a ran 22 ga wata a Lusaka, babban birnin kasar, cewar hukumar ta yi matukar farin ciki da ganin cewa, Zambia tana kokarin cika alkawarin da ta yi wajen daidaita harkokin 'yan gudun hijira, jama'ar Zambia kuma sun ba da babban taimakon kayayyaki ga 'yan gudun hijira 'yan asalin kasashen da ke makwabtaka da ita.
Haka kuma Madam Joyce ta ce, UNHCR za ta inganta hadin gwiwa tare da gwamnatin Zambia domin warware matsalar komawar 'yan gudun hijira fiye da dubu goma da ke zaune a Zambia cikin dogon lokaci ta hanyoyin samun gindin zama a wurin da kuma komawarsu gida bisa son rai.
Bugu da kari, mataimakin ministan harkokin cikin gida na kasar Zambia ya yi furuci a yayin taron, cewar gwamnatin Zambia za ta ci gaba da yin kokari wajen warware matsalar 'yan gudun hijira. Gwamnatin kuma za ta dauki matakai daban daban don tsugunar da su, kuma za ta nuna girmamawa ga zabinsu bisa son rai. Yanzu gwamnatin ta riga ta tsara shirye-shirye uku a wannan fanni, kamarsu komawarsu gida bisa son rai, da samun gindin zama a wurin da suke zaune yanzu, kana da tsugunar da su a sauran wurare.(Kande Gao)