Bisa kididdiyar da MDD ta yi, an ce, a halin yanzu, akwai mutane miliyan 4 dake bukatar taimakon jin kai a kasar Syria, yayin da kuma wasu miliyan 2 sun rasa gidajensu.
Bayan ganawar tasu, Jassim Zakaria ya bayyana cewa, an sami sakamako mai gamsarwa. To amma bai bayyana cikakken shirye-shiryen da bangarorin biyu suka tsara ba.
Tuni a wannan rana, Valerie Amos ta ziyarci wani wurin da ake kwantar da 'yan gudun hijira da ke birnin Damascus, inda ta nuna cewa, ziyarar ta wannan karo, ta fi mai da hankali ne kan ayyukan wasu tasoshin kiwon lafiya.
Wannan shi ne karo na uku da ta kai ziyara a kasar Syria bayan da kasar ta fada cikin rikici tun shekarar 2011, tana kuma shirya ganawa tare da ministan harkokin wajen kasar Syria. (Maryam)