Hukumar 'yan gudun hijira, ta sanar da cewa an samu wasu sabbin 'yan gudun hijira da su ka zo a yankin Elfoj da ke iyakar kasashen. Wadannan 'yan gudun hijira na tserewa ne sabili da tashin hankali da ke gudanan tsakanin dakarun gwamnatin kasar Sudan da kuma 'yan kungiyar People's Liberation Army a yankin Blue Nile na kasar.
An tabbatar da cewa, a halin yanzu akwai mutane sama da dubu 40 da ke kan hanya zuwa kasar Sudan ta kudu. Ganin cewa, 'yan gudun hijira na ci gaba da yin tururuwa zuwa sansanin 'yan gudun hijira na kudancin Sudan wurin ya kasance cikin wani hali mai kunci.
Hukumar 'yan gudun hijira ta MDD, ta sanar da cewa, babu wuri a halin yanzu a sansannin 'yan gudun hijira na Doro, ganin tun da farko 'yan gudun hijira dubu 37 ne ke a cikin sansannin. A bangaren sansannin 'yan gudun hijira na Jammam ana fuskantar matsalar ruwa duk da kokarin da ake na gina rijiyoyi.
Wannan tururuwa da 'yan gudun hijirar kasar Sudan ke yi zuwa yankin Upper Nile na kasar Sudan ta kudu, yana kunshe da mutane kimanin dubu 100. A yankin yammaci, jihar Unity na kunshe da wasu 'yan gudun hijirar guda dubu 38 daga jihar Fordofan ta kasar Sudan ta kudu. (Abdou Halilou).