A gun taron manema labaru da aka gudanar a wannnan rana, Maayatah ya bayyana cewa, kasar Jordan tana yin kokarin karba da tsugunar da 'yan gudun hijira daga kasar Syria, a halin yanzu, tana fuskantar da hali mai wuya.
Yayin da firaministan kasar Jordan Fayez Tarawneh yake ganawa da wakilin hukumar kula da harkokin 'yan gudun hijira ta MDD a wannan rana, ya nuna cewa, gwamnatin kasar Jordan za ta ci gaba da yin hadin gwiwa tare da hukumomin duniya dake da alaka da harkokin 'yan gudun hijira wajen tinkarar batun zuwan 'yan gudun hijira. Kana yana fatan za a kara samun taimako daga kasa da kasa.
Wakilin hukumar kula da harkokin 'yan gudun hijira ya nuna girmamawa da yabo ga kasar Jordan da take karba da tsugunar da 'yan gudun hijira daga kasar Syria, kana ya ce, hukumarsa za ta gudanar da wasu ayyuka bisa tushen girmama ikon mallakar kasar Jordan.
Bisa kididdigar da aka yi, yawan 'yan gudun hijira daga kasar Syria dake kasar Jordan a yanzu ya kai fiye da dubu 177, kana kimanin 'yan gudun hijira fiye da 1500 daga kasar Syria suke shiga kasar Jordan a kowace rana. (Zainab)