Sanarwar ta ce, tun bayan barkewar rikicin Sham har zuwa yanzu, 'yan gudun hijira fiye da dubu 200 sun tsare zuwa Turkiya daga Sham, kana wasu dubu 50 ko fiye da haka sun riga sun koma gida. Yanzu haka Turkiya ta gina sansanonin 'yan gudun hijira 13 domin saukar da mutanen da suka gudu zuwa Turkiya daga Sham.
Gwamnatin Turkiya ta bayyana sau da dama cewa, sakamakon tsanancewar halin da ake ciki a Sham ya sa 'yan gudun hijira suka yi ta kwarara zuwa Turkiya daga Sham, lamarin da ya dora wa Turkiya babban nauyi, har ma gwamnatin kasar ba ta da isassun kudaden tsugunar da wadannan 'yan gudun hijira, don haka tana fatan kasashen duniya za su ba da taimako don taimakawa wadannan 'yan gudun hijira.
An kiyasta cewa, ya zuwa karshen shekarar bana, yawan 'yan gudun hijira na Sham da ke yankin Gabas ta Tsakiya zai kai dubu 700. (Tasallah)