Madam Melissa Fleming, kakakin hukumar UNHCR ta bayyana a yayin taron manema labaru da aka yi a wannan rana cewa, hukumar ta kiyasta cewa, 'yan Mali fiye da dubu 400 za su gudu zuwa kasashen Nijer, Burkina Faso, Mauritaniya da wasu kasashen da ke makwabtaka da Mali nan da watanni da dama masu zuwa sakamakon tabarbarewar halin da ake ciki a kasar. Sa'an nan kuma, yawan al'ummar Mali da suka rasa wurin kwana zai karu da dubu 300 a cikin kasar.
Sabili da haka, hukumar UNHCR ta fara kara bai wa 'yan gudun hijira na Mali taimakon jin kai. Baya ga kara aikawa da ma'aikatanta zuwa Mali, hukumar ta kara yawan kayayyakin agaji da za ta tura zuwa kasar. (Tasallah)