Manyan sansanonin matsugunin 'yan gudun hijira guda biyu na kasashen Kenya da Habasha sun yi rajistan wassu sabbin 'yan gudun hijira 30,000 a farkon rabin shekarar nan kawai. Duk da cewar adadin yana kara hauhawa, ofishin kula da 'yan gudun hijiran ya ce, wannan sabon adadin ya nuna sassauci saboda tsananin rashin ruwan sama da kan kawo fari a wannan shekara a Somaliya ya ragu sosai kuma yanayin tsaro a wassu kasashen yanzu ana samun cigaba.
Sai dai kuma duk da haka akwai yiwuwar samun amfanin noma mara armashi a wata mai zuwa kuma yanayin zai fi kamari a kudanci da tsakiyar kasan, inda zai zama da tangal tangal amma hakan ba zai dore na lokaci mai tsawo ba. (Fatimah)