in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Saurin karuwar tattalin arzikin kasar Sin zai kai kashi 7.5 zuwa 8 cikin 100 a shekarar 2014
2013-11-14 16:16:11 cri
A ranar 13 ga wata, an yi taron tattaunawa dake da taken "Nazarin kasar Sin, don samun ci gaba" a kasar Singapore. A yayin taron, shehun malami a cibiyar nazarin raya kasa ta jami'ar Beijing, kuma mataimakin shugaban hadaddiyar kungiyar masana'antu da kasuwanci ta kasar Sin Lin Yifu ya yi jawabi kan babban taken taron, tare da amsa tambayoyin da wakilinmu ya yi masa.

Yayin da aka tabo maganar ko tattalin arzikin kasar Sin zai ci gaba da samun saurin bunkasuwa, Lin Yifu ya ce, duk da samun mummunan yanayi a waje, matsakaicin yawan karuwar tattalin arzikin kasar Sin, zai samu bunkasuwa da kashi 7.5 zuwa 8 cikin 100 a shekarar 2014.

A cewarsa da farko, akwai sauran rina a kaba wajen habaka sana'o'i da dama a kasar, da ci gaba da kyautata manyan ababen more rayuwa, kana kuma da kiyaye muhalli, don haka dukkan jarin da aka saka zai taimaka wajen bunkasuwar tattalin arziki, da raya zamantakewar al'umma matuka.

Lin Yifu ya ce, baya ga damar da kasar Sin take da shi na saka jari, kana akwai yanayin kudi da kasar ke ciki mai inganci. Yace yawan basusukan da Sin take bi musamman na kananan hukumomin kasar, ya kai kashi 48 cikin 100, cikin jimillar yawan kudaden da aka samu bisa ma'aunin tattalin arziki na GDP.

A ganin sa ko wace kasa, da basusukan da take bi ya gaza kashi 50 cikin 100, adadin ya yi kankanta, balle ma idan aka yi amfani da akasarin basusukan da kasar Sin take bi wajen saka jari. Har ila yau, jama'ar kasar Sin sun ajiye kudade da dama a banki, baya ga kudaden ajiya a kasashen waje na kasar Sin, da yawansu ya kai dalar Amurka biliyan 3700.

Idan aka yi la'akari da wadannan batutuwa, a iya cewa, tattalin arzikin kasar Sin zai ci gaba da samun karuwa, da adadin da ya kai kashi 7.5, zuwa 8 cikin 100 a shekara mai zuwa.(Bako)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China