A ran Alhamis 28 ga wata a nan birnin Beijing, aka bude taron dandalin tattaunawa kan hadin gwiwwa da raya masana'antu a tsakanin kasashen Sin da Afirka karo na uku, wanda kwamitin kula da dandalin tattaunawa kan raya masana'antu a tsakanin Sin da Afirka, da kuma kungiyar hadin kai a tsakanin Sin da Afirka suka shirya tare.
A lokacin taro mahalarta za su tattauna kan makomar hadin kan Sin da Afirka a fannonin cinikayya karkashin babban taken taron wato amincewa da juna da hadin kai, don samun bunkasuwa tare.
A cikin jawabinsa, babban sakataren kwamitin kula da dandalin tattaunawa kan hadin kai da raya masana'antu a tsakanin Sin da Afirka Mista Cheng Zhigang ya ce, tun lokacin da aka kafa dandalin, an ba da shawara ga kamfanoni fiye da 500.
Don haka in ji shi, taron dandalin tattaunawa na wannan karo zai sa kaimi wajen ganin bangarorin Sin da Afirka sun kara samun sabbin fannoni da hanyoyi wajen hada kansu.(Danladi)