An kaddamar da yankin cinikayya cikin 'yanci na gwaji a birnin Shanghai na kasar Sin a jiya Lahadi 29 ga wata. Kamfanoni na gida da na waje 36 ne suka sami iznin shiga wannan yanki.
Ministan kasuwanci na kasar Sin Gao Hucheng ya ce, wannan yanki ya kasance wani mataki ne na ba da tabbaci ga kyautata manufofi da kuma nazarin sabbin hanyoyin samun bunkasuwa da tattara sabbin fasahohi da hanyoyi game da ingiza tsarin yin kwaskwarima da bude kofa ga kasashen waje, Har ma yana da ma'ana sosai wajen kara samun bunkasuwar tattalin arziki da sauransu ta yadda za a cimma burin kafa wani yanki mai inganci cikin shekaru biyu zuwa uku, ta hanyar bin doka yadda ya kamata, da kuma samar da dama mai kyau wajen zuba jari, sannan da kai ga matsayin yanki dake biyan bukatun kasa da kasa. Ban da haka, za a daidaita aikin sarrafa da yin rigakafin hadarin cinikayya, da kuma kafa wani tsarin tattalin arziki mai yakini dake bude kofa ga kasashen waje.
A wannan rana kuma, kwamitin sa ido kan takardun mallakar abubuwa na kasar Sin da kwamitin sa ido kan inshora na kasar Sin da kuma kwamitin sa ido kan ayyukan bankuna na kasar Sin da sauran hukumomi sun gabatar da manufofin taimakawa wannan yanki. (Amina)